Dorewa da yin Ibadun da akayi a cikin watan Ramadan alamace ta imani – Farfesa Sani Musa Ayagi

images.jpeg
images.jpeg

Farfesa Sani Musa Ayage wanda shine limamin da ya ja sallar eidi na karamar sallah, a masallacin tsohuwar jami’ar Bayero dake jihar Kano, ya ja hankalin al’ummar Musulmai da su Dore da yin kyawawan halaye da ibadun da suka koya a cikin watan Ramadana.

Limamin ya kuma hore Musulamai da su dage tare da bada kulawa ga soyyayar Annabi Muhammad SAW, da yin ladabi a gareshi.

Ya kara da jan hankalin al’ummar Musulami da su daure su yi sallar Juma’a bayan gabatar da sallar eidi, domin yin hakan abu ne mai kyau wanda Allah yana son hakan.

“Ya jama’ar Musulmi yau ranace ta yafiya, ranace ta afuwa, mu sadar da zuminci a wannan rana, muyi Sadaka tare da yin sallarJuma’a, bayan sallar eidi, domin yau eidi biyu ne ya hadu, karkace don kayi sallar eidi bazaka kai ta Juma’a ba.”

A Karshe ya yi addu’ar samun zaman lafiya mai durewa a Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here