Zelensky ya gayyaci Tinubu ya ziyarci Ukraine bayan ya taya shi murna a matsayin shugaban Najeriya.

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy ya gayyaci zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci kasar da yaki ya daidaita bayan ya taya shi murnar lashe zaben 2023 a Najeriya.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito, ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ofishin zababben shugaban kasar ya fitar mai dauke da sa hannun Tunde Rahman.

Zelenskyy, a cikin wata wasikar taya murna da ya sanya wa hannu, ya bayyana jin dadinsa da yadda babban zaben Najeriya ya gudana cikin kwanciyar hankali, musamman ma ya yaba da nasarar da Tinubu ya samu a matsayin shugaban Najeriya, inda ya kara da cewa kasarsa ta kuduri aniyar kara karfafa hadin gwiwa da Najeriya.

Zelenskyy ya yi amfani da damar sakon fatan alheri wajen mika goron gayyatarsa ​​ga zababben shugaban kasar da ya ziyarci kasar Ukraine a ziyarar aiki da zarar ya hau karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Shugaban na Yukren ya rubuta: “Don Allah ku karɓi sakon taya murna ta bisa zaɓen ka a matsayin Shugaban Tarayyar Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here