Yan Sanda Sun Kama Uban Da Ya Yi Wa ’Yarsa Mai Shekara 5 Fyade

wp content uploads 2020 08 Police arrest man for Sodomy
wp content uploads 2020 08 Police arrest man for Sodomy

Wani magidanci da ya yi wa ’yarsa mai shekara biyar a duniya fyade ya shiga hannun ’yan sanda.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta kama magidancin mai shekara 28 ne bayan mahaifiyar yarinyar da aka sakaya sunanta ta kai karar mijin nata zuwa ofishin ’yan sanda

Kakakin rundunar, SP Abimbola Oyeyemi, ya ce mahaifiyar yarinyar ce ta kai kara caji ofis bayan ta lura yarinyar tana jin zafi a matucinta a duk lokacin da take yin fitsari ko ake yi mata wanka idan aka taba gabanta.

Hakan ne ya sa ta tistiye ’yar, wadda ta sanar da ita cewa mahaifinta ne ya kwanta da ita a lokacin da mahaifiyar ta fita unguwa.

Samun wannan korafi ya sa babban jami’in ’yan sanda (DPO) na Ijebu-Mushin ya tura jami’ansa suka kamo mutumi a ranar 22 ga watan nan na Mayu, kuma bai musanta yin lalata da ’yar tasa ba.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun, Olanrewaju Oladimeji ya bayar da umarnin a tura mutumin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) domin ci gaba da bincike.

(Aminya)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here