A ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya soke ziyarar da ya kamata ya kai jihar Zamfara.
An soke ziyarar ne saboda rashin kyawun yanayi, a cewar gwamnan Zamfara Bello Matawalle.
Gwamnan ya ce shugaban shugaba Buhari ya kamata ya tashi daga Sokoto a cikin jirgi mai saukar ungulu zuwa Zamfara, amma ya fasa saboda rashin kyawun yanayi.
A cewarsa, “Shugaban kasa ya yi magana da ni kuma ya bukace ni da in isar da uzurinsa ga mutanen jihar.
Shugaban ya ce a mako mai zuwa zai sake shirya ziyarar zuwa jihar kuma za a sanar da mutane ranar da aka kayyade.
Wasu daga cikin shugabannin tsaro a yanzu haka suna Katsina amma ba za su iya tashi zuwa Zamfara ba saboda wannan dalili.
A kan haka ne muke mika uzurinmu ga al’ummar jihar kan dage ziyarar da aka yi saboda abin da ya fi karfin mu. a cewar gwamna Matawalle.
A ranar Alhamis ne Buhari ya kaddamar da kamfanin siminti na a Sokoto.
Shugaban ya samu rakiyar Gwamnan jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal; Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefele; Shugaban rukunin BUA, Alhaji AbdulSamad Rabi”u da shugaban kamfanin Max Air, Alhaji Dahiru Bara’u Mangal da sauransu.













































