Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Mista Usman Baba ya umurci kwamishinonin ‘yan sanda a fadin kasar nan da su kaddamar da kwamitocin tuntuba tsakanin hukumomin da ke kula da harkokin zabe.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar CSP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Baba ya ce, an ba da umarnin a sanya masu ruwa da tsaki wajen samar da dabarun dakile barazanar da ake fuskanta a babban zaben 2023.
Don haka, Alkali Baba ya umurci kwamishinonin Yan sanda da su yi aiki tare da dukkan membobin kwamitin don magance barazanar tashe-tashen hankula na siyasa da kuma tabbatar da gaggauta gurfanar da masu karya dokokin zabe.
Ya kuma ce an yi hakan ne domin tabbatar da tsaro da tsaron ma’aikatan hukumar da kayan aiki kafin babban zabe da lokacin da kuma bayan babban zabe.
Haka zalika, Sufeton ya ba da umarnin rarraba sabbin na’urorin kayan yaki da kayan kariya ga ‘yan sanda a duk fadin kasar don shirye-shiryen zaben.













































