Osun: Adeleke ya garkame asusun Gwamnati tare da warware nade-naden da Oyetola ya yi

Ademola Adeleke taking oath of office in Osun State 678x430 1
Ademola Adeleke taking oath of office in Osun State 678x430 1

A ranar Lahadin da ta gabata ne sabon gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya soke dukkan nade-naden mukamai da magabacinsa Gboyega Oyetola ya yi.

A jawabinsa na farko a ranar Lahadi Adeleke, tsohon dan majalisar dattawa, ya ce tsohon gwamnan ya dauki matakai da dama a kwanakin baya na mulki wadanda jihar ba tare da kudaden gudanarwa.

An bayar da kwangiloli daban-daba cikin gaggawa ga masu laifi ba tare da tanadin kasafin kuɗi ba.

Adeleke ya kuma ba umarnin garkame duk asusun gwamnati a bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi tareda gaggauta kafa kwamitin da zai gudanar da kididdiga da kwato dukkan kadarorin gwamnati.

Idan dai za a iya tunawa tsohon gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola ya nada sakatarorin dindindin guda 30 kwanaki biyu kafin karewar wa’adinsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here