Gwamnan jihar Osun Sanata Ademola Adeleke da mataimakinsa, Kola Adewusi sun karbi rantsuwar kama aiki.
Babban alkalin jihar, Mai Sharia Adepele Ojo ya rantsar da mutanen biyu a wani gangamin taron da ya gudana ayau.
Ademola Adeleke ya shigo wurin taron ne bisa ayarin motoci da misalin karfe 11:20 na safe kuma ya kammala karban rantsuwa da karfe 11:50 na safe.
Wadanda suka halarci taron rantsuwar a filin wasa na birnin Osogbo sun hada da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da gwamnan jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom.
Sauran sune Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto, Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa, da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi.
Haka kuma a wurin taron an samu halartar uwargidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Titi Atiku, Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, da tsohon gwamnan Oyo, Cif Rashidi Ladoja, da dai sauransu.













































