Gwamnan CBN na neman karfafa dangantakar tattalin arziki da Gabas ta tsakiya

Cardoso in Saudi Arabia 750x430

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Olayemi Cardoso, ya bayar da shawarar karfafa dangantakar tattalin arziki da yankin gabas ta tsakiya da kuma al’ummar Najeriya mazauna yankin.

Cardoso ya yi magana ne a ranar Litinin a wajen wani taro da mataimakin gwamnan kan harkokin kudi na babban bankin kasar Saudiyya (SAMA), Talal Al-Humond, da aka gudanar a gefen taron kaddamar da tattalin arzikin kasuwanni masu tasowa, wanda ma’aikatar kudi, Saudiyya da ofishin shiyya na asusun lamuni na duniya (IMF) suka shirya a Riyadh.

Cardoso wanda ya bayyana cewa, akwai darussa da za a koya daga kasar Saudiyya ta fuskar raya ababen more rayuwa da yawon bude ido, ya ce, sadaukarwar da Saudiyya ta yi na habaka tattalin arzikinta ta hanyar sabbin ayyukan muhalli, da manyan sauye-sauye da kuma zuba jarin yawon bude ido na da matukar muhimmanci ga ci gaba.

Karin labari: Kotu ta hana CBN da wasu mutane yin katsalandan a kuɗaɗen ƙananan hukumomi

Ya kuma jaddada aniyar sa na hada kai da al’ummar Najeriya mazauna yankin gabas ta tsakiya domin inganta harkokin kudi da kuma karfafa bangaren kudi da Najeriya.

Ya bayyana cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) zai ci gaba da inganta tsarin tattalin arziki don samar da yanayi mai dacewa da zai saukaka ci gaban kamfanoni masu zaman kansu da samar da ayyuka masu inganci ga ‘yan Najeriya.

A martanin da ya mayar, Talal Al-Humond ya tabbatar wa Cardoso cewa babban bankin kasar Saudiyya zai yi aiki tare da babban bankin kasar CBN don ganin an cimma manufofin da za su dace da juna.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here