Zaman sauraron karar da tsoffin kwamishinonin Jihar Kano suka shigar kan kwace motocin aiki na gwamnati, wanda aka shirya a ranar Talata, bai gudana ba kamar yadda aka tsara.
Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa kotun a ranar Talata ta dage sauraron karar ne saboda dage dukkan kararrakin da aka sa wa ranar sauraro cikin wannan mako gaba daya.
Wani jami’in kotun ya bayyana cewa, “Duk kararrakin da aka tsara a wannan mako an dage su, yanzu an sa ranar 25 ga Mayun shekarar nan ta 2026 don sauraron karar kwamishinonin,”
Dagewar ta baya-bayan nan ta biyo bayan zaman da Kotun Ma’aikata ta Kasa ta yi a baya, karkashin jagorancin Mai Shari’a Mahmood Abba Namtari, inda aka fara sa ranar 28 ga Afrilu, 2026 don sauraron karar.
A wancan zaman, kotun ta kuma yanke tarar Naira 200,000 kan wadanda ake kara a kowace daga cikin kararraki biyar da ke da alaka bayan lauyan su ya nemi a dage zaman don ba su damar shigar da takardun da suka dace.
Lauyan Gwamnatin Jihar Kano, Barrista S. U. Jibril, ya shaida wa kotu cewa an sanar da shi a kure kusa da lokacin zaman kawai, kuma yana bukatar karin lokaci don shirya takardun da ake bukata.
Sai dai, lauyan tsoffin kwamishinonin, Suraj Sa’ed, SAN, ya amincewa da dagewar ba amma ya roki kotu ta yanke tara, yana mai jayayya cewa wadanda ake kara sun samu isasshen lokaci don ba da amsa kan karar.
Mai Shari’a Namtari, yayin da yake amincewa da dagewar, ya yanke tara kan wadanda ake kara kuma ya ba da umarni a saurari karar a sabuwar ranar.
Tsoffin kwamishinonin da suka shigar da karar su ne Dr. Yusuf Ibrahim K/Mata, AVM Ibrahim Umar (Mai Murabus), Nasir Sule Garo, Adamu Aliyu Kibiya da Mustapha Rabi’u Kwankwaso, suna neman hana Gwamnatin Jihar Kano kwace motocin gwamnati da aka ba su a lokacin da suke aiki a matsayin kwamishinoni.
Sun sanya babban lauyan jihar Kano, Gwamnan Jihar Kano da Hukumar Korafe-Korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano a matsayin wadanda suke kara.











































