Hatsarin kwale-kwalen Borgu: Gwamnatin tarayya za ta samar da tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa

154 feared dead in Kebbi boat mishap (2)

Gwamnatin tarayya ta ce, ta hannun hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) za ta bayar da tallafin da ya dace ga iyalan wadanda hatsarin kwakwalen Borgu ya shafa da kuma wadanda suka tsira a Neja.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu, ya ce gwamnati ta samu wannan labari mai cike da bakin ciki da tashin hankali.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, yayin da jirgin ruwan Borgu ya afku a karamar hukumar Borgu da ke Neja a ranar Talatar da ta gabata ya lakume rayukan mutane 32, kimanin mutane 50 kuma aka ceto.

Karin karatu: Ambaliyar ruwa: Kano na shirin samar da sabon tsarin magudanar ruwa – Mahukunta

A cewar Idris, ibtila’in ya zo ne watanni kadan bayan da wata mummunar ambaliyar ruwa ta yi barna a garin Mokwa da ke cikin Neja.

Ya kuma ja kunnen ‘yan kasar cewa, babu wanda ya isa ya shiga tafiye-tafiyen kwale-kwale ba tare da sanya rigar kariya da ta dace ba, ya kara da cewa matakan kariya na taimakawa tsakanin rayuwa da mutuwa. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here