Kano: Babbar jojin jihar ta saki fursunoni 6 da suka ɗauki dogon lokaci a gidan yari

IMG 20250905 WA0012 750x430

Babbar jojin jihar Kano, Mai shari’a Dije Audu Aboki, ta bayar da umarnin sakin fursunonin shida da suka dade a gidan yari a ziyarar aikin da ta kai gidajen yari a fadin jihar.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali na jihar Kano, CSC Musbahu Lawan K/Nasarawa ya fitar ranar Juma’a.

A cewar sanarwar, mutanen da aka saki sun kasance a gidan yari na tsawon lokaci saboda ci gaba da shari’a, da baita kotu bayanan shari’a, da kuma rashin gurfanar da su a gaban kotu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mai shari’a Aboki ta bayyana matakin ne a matsayin wani yunkuri na ci gaba da daukar matakan dakile cunkoso a cibiyoyin da ake tsare da su da kuma magance tsaikon da ake samu a harkokin shari’a.

Karanta: Ambaliyar ruwa: Kano na shirin samar da sabon tsarin magudanar ruwa – Mahukunta

Ta kuma ƙarfafawa fursunonin da aka saki su rungumi canji mai kyau kuma su zama kafu na gari a cikin al’umma. “Yanzu kuna da damar fara sabuwar rayuwa, ku zama jakadun zaman lafiya kuma ku guji aikata laifuka,” in ji ta.

SolaceBase ta ruwaito cewa shi ma da yake magana a yayin ziyarar, Kwanturolan hukumar na jihar Kano, Ado Inuwa, ya gargadi fursunonin da aka sako kan kada su koma aikata laifuka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here