Bullar Sautin Murya: Mara sa kishi Ne Ke kokarin Yi Mana Ingiza Mai Kantu Ruwa – Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar kano ta bukaci jama’a da su yi watsi da yunkurin da kafafen sada zumunta na intanet ke yi ga wata tattaunawa ta wayar targarahu tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Kabiru Masari, dan takarar mataimakin shugaban kasa kan dangantakar sa da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa an sami karin gishiri kan wannan faifan bidiyo ne a kokarin haifar da rashin jituwa tsakanin ‘yan siyasar biyu.

Sanarwar ta bayyana cewa, “daga dukkan alamu, wasu mutane ne marasa kishi me daukar nauyi yada wannan kanzon kurege.

‘’Sai dai kwamishinan ya yi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC da sauran jama’a da su yi watsi da irin wannan yunkurin kuma su kwantar da hankalinsu da biyayya ga jam’iyyar domin ganin an yi nasarar rantsar da zababben shugaban kasa.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne wani faifan bidiyo ya karade shafukan sada zumunta inda aka jiyo sautin wayar tarho tsakanin Gwamna Ganduje da Ibrahim Masari, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar APC, inda gwamnan yake kokawa kan yadda “shugaban kasa ya yi masa rashin adalci” inda ya gana da Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP.

An kuma ji Gwamnan yana cewa lissafin da Tinubu ya yi na ganawa da Kwankwaso ba mai bullewa ba ne.

Tinubu da Kwankwaso sun gana na tsawon awanni hudu a kasar Faransa, inda suka tattauna batutuwa da dama.

Wannan lamari na ci gaba da tada ƙura kuma ya zama zance mafi shura a bakunan jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here