Gwamnatin Tarayya Da Kungiyar Likitoci Masu Yajin Aiki Sun Rattaba Hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna.

Likitocin masu Neman kwarewa da ke yajin aiki da kungiyar likitocin Najeriya (NMA) sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatin tarayya kan yajin aikin da suka fara a ranar Laraba.

Da suke gudanar da sanya hannun, kungiyar likitocin tace, likitocin da ke yajin aikin sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar ne domin tauna aya a bukatarsu na a inganta musu yanayin aiki.

Kakakin ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, Mista Olajide Oshundun, ya bayyana cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar a ofishin ministan, Mista Chris Ngige.

“Wannan zama anyi shi ne da nufin dakatar da yajin aikin,” in ji shi.

Likitocin na kuma neman ayi musu kari kai tsaye a Tsarin Albashin su wanda zai kai kashi 200 cikin 100 na yawan albashin likitoci a halin yanzu.

Likitocin da ke yajin aikin sun kuma bukaci a sake duba Tsarin Albashin su wanda aka yi nazari a karshe a shekarar 2009 da kuma biyan bashin albashin da ba a biya ba na shekarar 2014 zuwa 2016.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here