Wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi wa wata mata ‘yar shekara 80 fyade ta mutu har lahira a garin Ore da ke karamar hukumar Odigbo a jihar Ondo.
Mummunan lamarin da ya faru a cikin gonar ta da ke yankin Costain a cikin Ore ya haifar da fargaba a tsakanin jama’ar yankin.
Wani dan unguwar da ya zanta da manema labarai ya ce, wadda aka kashe ta yi batan dabo ne kwanaki bayan ta tafi gona ne kawai aka ga gawarta yashe.
Rahotanni sun bayyana cewa da farko an yi mata tsirara ne bayan da maharan suka yi mata fyade.
Wata majiya a garin ta ce, “Wannan ba shi ne karon farko da muke ganin wannan mummunan al’amari ba, an yi wa mata da dama fyade a gonakinsu da wasu barayin da ake zargin makiyaya ne.
Majiyar ‘yan sandan ta ce daga baya wanda ake zargin ya kai matasan inda aka gano gawar wadda aka kashe inda ya yi zargin cewa wasu makiyaya ne suka kashe ta.













































