Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da sake sauyawa kwamishinoninsa guda uku ma’aikatu a wani sauyi da ya yiwa majalisar zartarwarsa domin inganta shugabanci nagari.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da Al’adu Sagir Musa ne ya bayyana hakan a karshen taron majalisar zartarwa ta jiha a ranar Litinin a Dutse.
Ya ce sauye-sauyen na da matukar muhimmanci domin bunkasa kokarin gwamnatin da ke da nufin tabbatar da ci gaba mai dorewa a jihar.
Wadanda abin ya shafa sun hada da Muhammad Alhassan na ma’aikatar kasa, gidaje da raya birane da tsare-tsare inda aka mayar da shi zuwa ma’aikatar albarkatun ruwa, sai Ibrahim Hanungiwa na ma’aikatar kananan hukumomi da ci gaban al’umma zuwa ma’aikatar albarkatun ruwa.
Karin karatu: Yan sanda sun kama wani matashi dan shekara 20 da ya kashe mahaifinsa a Jigawa
Yayin da Ahmed Garba ya koma ma’aikatar kananan hukumomi da ci gaban al’umma ma’aikatar filaye, gidaje, raya birane da tsare-tsare na yankin.
Musa ya ce sauye-sauyen sun fara aiki nan take, inda ya ce ana sa ran jami’an da abin ya shafa za su kai rahoto ofishinsu nan da ranar 19 ga watan Mayu (NAN).