
Wani matashi dan shekara 20 mai suna Muhammad Salisu ya kashe mahaifinsa Salisu Abubakar da adda a karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Shi’isu Adam ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Litinin a unguwar Bakin Kasuwa da ke gundumar Sara.
Sanarwar ta ce wanda ake zargin ya kai wa mahaifinsa hari da adduna, inda ya yi masa munanan raunuka a kafadarsa, da wuyansa, da kuma kirjinsa.
“An garzaya da wanda aka kashe zuwa cibiyar kiwon Lafiya ta tarayya, Birnin Kudu, domin a kula da lafiyarsa, amma abin takaici, Likitan ya tabbatar da mutuwarsa,” in ji shi.
“Daga baya an bada gawar ga ‘yan uwa domin binne shi,” in ji Adam.
Karin karatu: Yanzu-yanzu: EFCC ta bada belin VeryDarkMan, ta sanar da dalilan kama shi
Sai dai Adam ya tabbatar da cewa an kama wanda ake zargin Salisu, kuma an kwato addar daga hannunsa.
A cikin sanarwar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, AT Abdullahi, ya bayar da umarnin a mayar da shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuffuka na jihar da ke Dutse domin gudanar da sahihin bincike.
“Bayan an kammala bincike, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar cikakken hukuncin doka.
Adam ya kuma kara da cewa har yanzu ba a gano musabbabin kisan gillar ba, kuma ‘yan sanda na binciken musabbabin faruwar lamarin.