Gwamnatin Amurka ta amince ta sayarwa da Turkiyya sabbin jirajen yaƙi guda 40 kirar F-16 kan kuɗi dalar Amurka biliyan 23 – wani ciniki da aka jima ana jira wanda ya zo bayan Turkiyya ta amince da Sweden ta zama mamba a Nato.
Cikin yarjejeniyar har da sayar da kayan gyaran wasu jirage 79 irin wanda za ta sayan, wadanda take da su tun tuni.
Ma’aikatar harkokin waje ta Amurka ta shaida wa Majalisar dokokin ƙasar cewa ta amince da sayarwa Girka jirage 40 ƙirar F-35 itama, da suka kai darajar dala biliyan 8.6.
Karanta wannan: Gwamnatin Kano ta gargadi shugabannin kananan hukumomi kan siyar da kadarorin gwamnati ba bisa Ka’ida ba
Turkiyya ta amince da Sweden ta zama mamba a Nato bayan sama da shekara guda tana jan ƙafa saboda rashin jituwa da ke faruwa tsakanin ƙawayen ƙasashen.
Majalisar dokokin Turkiyya ta amince da Sweden ta zama mamba ne a wannan makon, bayan shugaba Tayyib Erdogan ya amince da buƙtar.
Kuma nan take shugaba Biden ya amince da asayar da jiragen.
Tsokaci akan Amurka ta sayarwa da turkiya jiragen yaki. Ni a ganina Kara hura wutar rikici ce akan Russia da sauran kasashen da ke kewaye da ita. Musamman Sweden, Ceprus, Azerbaijan, da sauransu.