Yanzu-yanzu: Sarkin Musulmi ya bukaci a fara duban jinjirin watan Ramadan

d6764bb9 ee43 48f7 9b16 7874af898bf5 e1663538043755

Majalisar Sarkin Musulmi ta bukaci al’umma da su fara duban jinjirin watan Ramadan daga ranar Juma’a 28 ga Fabrairun 2025

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Wazirin Sokoto kuma shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na Majalisar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaidu.

Sanarwar ta bukaci al’ummar Musulmi da su lura da ganin jinjirin wata a ranar Juma’a kuma su kai rahoto ga Hakimin gundumarsu ko Kauye mafi kusa don tuntubar mai alfarma sarkin musulmi da shugaban majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta Muhammad Sa’ad Abubakar domin sanar da jama’a.

Karin karatu: Taron mahaddata Kur’ani: Sarkin Musulmi ya sanar da dalilan ɗage taron

SolaceBase ta ruwaito cewa sanarwar ta kara da cewa idan aka ga jinjirin watan, za a iya tuntubar wadannan lambobin waya don sadarwa ga Majalisar Sarkin Musulmi:

08037157100

08066303077

08035965322

08099945903

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here