An saki magoya bayan Arsenal da aka kama kan wasansu da Manchester United

FB IMG 16746361024753676
FB IMG 16746361024753676

An saki magoya bayan Arsenal takwas da aka kama a garin Jinja na Uganda, lokacin da suke murnar nasarar da ƙungiyarsu ta samu a wasan hamayya da Manchester United a gasar Premier Ingila.

Lokacin da aka kama su a ranar Litinin, suna sanye da rigunan Arsenal da kuma wani kofi a hannunsu.

‘Yan sanda sun ce babu wanda ya basu umarnin yin wannan murna wadda za ta iya haifar da rikici a cikin al’umma.

Kakakin ‘yan sanda na yankin James Mubi, yace bayan wata tattaunawa da aka yi tsakanin jami’an tsaro, an amince a sake su kowa ya kama gabansa amma an ginda ya musu sharuɗa.

Ɗaya daga cikin magoya bayan ya faɗawa ‘yan jarida cewa “sun nemi umarni gabanin wannan murna da suka gudanar da nasara kan Man United”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here