Najeriya ta gamu da cikas a ƙoƙarinta na neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya na baɗi, bayan da ta tashi 1-1 da Zimbabwe.
Victor Osimhen ne ya fara ci wa Najeriya kwallo a minti na 74 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo.
Read also: AFCON: Mutane 8 sun mutu, da dama sun jikkata a yayin wani turmutsutsu
Sai dai Zimbabwe ta farke ana daf da tashi a minti na 90 ta hannun ɗan wasanta na gaba, Taranda Chirewa.
Read also: Arsenal ta yi kunnen Doki da Chelsia da ci 1-1
Wannan sakamako na nufin cewa Najeriya na mataki na huɗu a rukunin C, inda Ghana ke gabanta a matsayi na ɗaya da kusan ratar maki shida bayan buga wasanni shida.
Read also: An sauya Fasalin gasar cin Kofin Zakarun Turai UEFA
Wasan da Najeriya za ta yi Bafana Bafana a watan Satumba, zai kasance mai matukar muhimmanci – Ganin cewa ƙasar da ke saman kowane rukuni ne kaɗai ke samun damar zuwa gasar kofin duniya.












































