Hukumar Kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, ta sanar da sabon tsare tsare na gasar cin kofin zakarun Turai UEFA wato champions league daga shekarar 2024/25.
A sabon tsarin da hukumar ta amince da shi, zai fara aiki daga shekarar gasar zata kunshi kungiyoyi 36 maimakon 32 da yake a yanzu.
Kazalika tsarin ya soke jadawalin rukuni inda za a fafata kai tsaye, ko wacce kungiya zata kara da ko wacce.
Haka kuma ko wacce kungiya zata buga wasanni takwas a gasar , inda a gefe guda kuma za a bawa kasashe biyu da suka yi kokari a gasar karin kungiyoyi biyu a gasa ta gaba.