Zakaran damben duniya Mayweather ya kawo ziyara Nigeria

IMG 20220511 WA0019
IMG 20220511 WA0019

Tsohon gwarzon Dan wasan dambe na Duniya, da ya yi murabus Dan Kasar Amurka Floyd Mayweather Junior, ya kawo ziyara Nigeria.

A ziyarar ta sa ranar Litinin 09 ga Mayu 2022, ya gana da ministan sufuri Rotimi Amaechi, tare da yin alkawarin samar da makarantar wasan dambe a Kasar.

Tsohon zakaran wasan ajin masu nauyin ya bayyana hakane yayin tattaunawar sa da manena labarai a birnin tarayya Abuja.

Ana sa ran tsohon Dan wasan zai tattauna da jami’an hukumar wasan Dambe ta Najeriya domin bada shawarwari tare da kulla Alaka don habakka wasan a fadin Kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here