Dalibai bakwai a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kwara da ke Ilorin sun samu raunuka daban-daban yayin da wata gobara ta tashi a wani gidan sayar da iskar gas da ke kusa da dakin kwanan dalibai.
An tattaro cewa gobarar ta afku ne a Destiny Villa, titin Dola Abimbola, unguwar Elekoyangan a karamar hukumar Ilorin ta Gabas da yammacin ranar Asabar.
Har ila yau, an ce ma’aikaciyar gidan mai ta samu rauni a lokacin da lamarin ya faru.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Hakeem Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin da ta gabata.