A ranar Talata ne tsohon shugaban karamar hukumar Kiyawa a Jam’iyyar APC Malam Isyaku Adamu ya sayi Fom din tsayawa takarar Majalisar Wakilan Tarayya kan kudi naira miliyan 10.
Taohon shugaban karamar hukumar ta Kiyawa, ya sayi Fom din ne bayan kiraye-kirayen ‘Yan Jam’iyyar su, ‘Yan uwa, da abokan arziki na ya fito ya nemi takarar Majalisar wakilan tarayya da zai wakilci Mazabun Kiyawa da Dutse, a zaben shekarar 2023.
A baya dai wasu jiga-jigan jam’iyyar ta APC wadanda suka hada da tsohon Dan-Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabun Kiyawa da Dutse Tijjani Ibrahim Ghaya, da Shugaban Jam’iyyar APCin Karamar hukumar Alhaji Abdullahi Hassan da shugabannin Mata da Matasa da kungiyoyin Sa kai su ne suka rinka kiraye-kirayen ya tsaya takarar domin ci gaba da ayyukan da ya samo lokacin yana shugabantar karamar hukumar.













































