Rundunar ‘Yan San jihar Jigawa ta haramtawa Direbobi yin Lodin da ya wuce Kima

IMG 20210831 WA0068
IMG 20210831 WA0068

Rundunar ‘Yan sandan Jihar Jigawa ta umarci daukacin Jami’an ‘Yan sanda dasu Fara Kamawa tare da hukunta direbobin dake Lodin da ya wuce kima da kuma tukin ganganci, a Fadin Jihar.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, CP Aliyu Sale Tafida, ne ya bada Umarnin yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a birnin Dutse.

Aliyu Tafida, ya kara da cewa kasancewar kare rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne aikin rundunar hakan yasa shi bada umarnin.

“Aikin mu ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma don haka baza mu bari wasu mutane su rinka wasa da rayukan al’umma ba ta hanyar yin lodin da ya wuce kima ko kuma gudun wuce sa’a.” Inji Kwamishinan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here