An tabbatar da labarin rasuwar Olunloyo a cikin wata sanarwa da aka fitar a Ibadan a safiyar Lahadi ta hannun Oladapo Ogunwusi, a madadin iyalan marigayin.
Olunloye, wanda ya kasance gwamnan jihar Oyo tsakanin 1 ga Oktoba zuwa 31 ga Disamba, 1983, a karkashin jam’iyyar NPN ta lokacin, ya rasu kwanaki kadan ya cika shekaru 90 a duniya.
“Muna sanar da rasuwar Dr Victor Omololu Olunloyo, tsohon gwamnan jihar Oyo, masanin lissafi kuma injiniya, kuma mashahurin masanin fasaha”.
“Balogun na Oyo da Otun Bobasewa na Ife, Olunloyo shi ne shugaban farko na kwalejin fasaha ta Ibadan kuma shugaban farko na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara, da sauran mukamai.
“Tasirin da ya yi na hidima ga kasa da kuma bil’adama abin alfahari ne ga iyalinsa da abokan zamansa.