Hukumar tace fina-finai ta Kano ta gayyaci mawaƙi Tijjani Gandu kan zargin karya ƙa’ida

IMG 20261004 WA0013 750x430
  • Hukumar tace gina-finai da ɗab’i ta Jihar Kano ta gayyaci mawaƙi Tijjani Gandu domin ya bayyana a gabanta kan zargin keta ƙa’idojin hukumar da ake danganta shi da sakin wata sabuwar waƙa.

Hukumar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Juma’a, a madadin Sakataren Zartarwa na hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha.

A cewar sanarwar, ana buƙatar mawaƙa, marubuta da sauran masu samar da ayyukan adabi da fasaha su kai waƙoƙi, rubuce-rubuce da sauran ayyukansu ga hukumar domin tantancewa da amincewa kafin su fitar da su ga jama’a.

Ta ce ana gudanar da wannan tantancewa ne domin tabbatar da cewa ayyukan fasahar da ake wallafawa ba su ƙunshi kalmomi, maganganu ko saƙonnin da ka iya tayar da rikici a tsakanin jama’a ko kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma ba.

SolaceBase ta ruwaito cewa hukumar ta ce dokar da ta kafa ta ta bata ikon tantancewa da kuma sanya dokoki kan waƙoƙi da sauran abubuwan da suka dace da ake samarwa ko yaɗawa a yankin da ke ƙarƙashin ikonta.

Ta jaddada cewa mutane ba za su iya yin watsi da ƙa’idojin hukumar da gangan ba da sunan amfani da ’yancin faɗar albarkacin baki.

“Hukuma ba za ta bari mutane su yi watsi da ƙa’idojinta da gangan ba da sunan amfani da ’yancin faɗar albarkacin baki.”

Hukumar ta kuma sake jaddada aniyarta na tabbatar da doka da oda yayin gudanar da ayyukan da aka ɗora mata na sanya ido, inda ta tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa za a aiwatar da ƙa’idojinta cikin adalci, ba tare da nuna wariya ko fifita wani ba.

Don haka, hukumar ta buƙaci Gandu da ya mutunta doka tare da amsa gayyatar da aka yi masa ta hanyar bayyana a gabanta.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa rashin amsa gayyatar na iya zama rashin bin doka, kuma hakan na iya sa a ɗauki ƙarin matakai a kansa bisa tanadin ƙa’idojin da suka dace.

Haka kuma, ta yi kira ga mawaƙa, marubuta da sauran masu ruwa da tsaki a masana’antar fasaha da su ci gaba da bin ƙa’idojinta, tana mai cewa bin ƙa’idojin na da muhimmanci wajen inganta zaman lafiya, tsari da ci gaban Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here