Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin kasa (CBN), Dr Kingsley Moghalu, ya yi watsi da sanya sunansa a cikin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis, kwararren masanin tattalin arzikin ya ce jam’iyyar ba ta tuntube shi ba kafin ta sanya shi a cikin tawagar yakin neman zaben tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.
Read also: Labour Party takori Doyin Okupe da karin wasu
Tun da fari Atiku ya fitar da jerin sunayen kwamitin yakin neman zaben, inda ya nada Kashim Ibrahim Imam a matsayin shugaba da Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna a matsayin mataimakin shugaba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya sanya Moghalu a cikin kwamitin manufofin yakin neman zabe, karkashin jagorancin Mohammed Hayatu Deen, wanda ya tsaya takarar fidda gwanin shugaban kasa a ADC tare da Atiku.
Atiku ya ce mambobin kwamitin manufofin za su samar da amsoshi masu amfani ga matsalolin da ‘yan Najeriya suka gabatar a yakin neman zaben.
Sai dai, Moghalu ya ce ADC ba ta nemi yardarsa ba kafin ta sanya sunansa a cikin jerin.
Read also: INEC ta sanar da ranar gudanar da zabukan gwamnonin Ekiti da Osun
“Na yi mamaki da na ga wata sanarwa daga tawagar yakin neman zaben @atiku da @ADCNig da ta sanya sunana a matsayin memba a kwamitin manufofin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar don yakin neman zaben shugaban kasa na 2027,” ya rubuta.
“Don a fayyacewa, ba a tuntube ni ba kuma anemi amincewa ta ba don a wallafa sunana a matsayin memba a kwamitin manufofin dan takarar ADC.
“A hakikanin gaskiya, ni ba memba bane na kwamitin manufofin Atiku, koda kuwa ba a hukumance ba ko a kowane matsayi na ba da shawara.”
Moghalu ya ce ya bar siyasar jam’iyya a Najeriya tun 2022 kuma ya ci gaba da rike matsayinsa na rashin son kai a harkokin kasar.
“Babban aikina shi ne a matsayin Shugaban @IGETAfrica, cibiyar mai zaman kanta da ba ta jam’iyya ba da kuma shugabanci makarantar ilimi, kuma a matsayin Shugaban Sogato Strategies, wani kamfani mai ba da shawara kan hadarin siyasa da dabarun tsari.”
Read also: Abba Gida Gida ya maka shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano a kotu bisa kalaman tunziri
Moghalu ya ce ya ci gaba da jajircewa ga kasar da ci gabanta, “amma irin wannan jajircewa ba lallai ba ne ya kunshi wata alakar jam’iyya.”
“Na dauki hanyar dattaku, ba bangaranci ba,” ya kara da cewa.












































