Kamfanin KEDCO ya nada sabon shugaban sashin sadarwa

IMG 20221201 WA0198
IMG 20221201 WA0198

Kamfanin Rarraba hasken wutar Lantarki ta Kano ya nada Sani Bala Sani a matsayin sabon sashin sadarwa na kamfanonin.

Jaridar Solacebase ta rawaito ta cewa nadin nasa wani bangare ne na kokarin samun ingantaccen aiki mai tasiri na kamfanonin.

Kafin nadin nasa Sani, ya rike mukamai da dama a bangarorin shugabanni daban daban, inda ya jajirce wajen samar da ayyukan jin dadin jama’a ta hanyar bada tallafi ga mata a kauyukan Dausayi, Dausara da Dankunkuru a jihar Kano.

Ya kuma jagoranci bayar da tallafi ga sansanonin ‘yan gudun hijira da ke Kiyawa, jihar Jigawa da panshekara a Kano duk a kokarinsa na inganta martabar kamfanin na KEDCOs da manufofin sa kai na abokan ciniki.

Kwarewar Sani Bala a harkokin hulda da jamaa ya taimaka matuka wajen ganin KEDCO ta zama zakara a matsayin wanda ya lashe lambar yabo ta bangaren wutar lantarki karo na 7 na Africa, inda Kano DISCO ta doke Safi Analytics da Senegalese National Electricity.

Kafin nada shi, Sani ya yi aiki a matsayin mukaddashin shugaban sashen sadarwa na kamfanin na tsawon shekaru 5.

Sani ya kammala karatunsa na digiri a Jami’ar Usmanu Dan-Fodio da ke Sakkwato da Jami’ar Salford da ke birnin Manchester na kasar Birtaniya ya yi digirin digirgir a fannin Harsuna, inda ya karanci Turanci da kuma da digiri na 2 a fannin Hulda da Jama’a da Duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here