YANZU-YANZU: Kotu ta soke tsayawa takarar Andy Uba a zaben gwamnan Anambra

AC42BBA1 B88D 4EA2 80A6 72137364F0C4
AC42BBA1 B88D 4EA2 80A6 72137364F0C4

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja  soke tsayawa takarar Sanata Andy Uba a zaben gwamnan jihar Anambra da aka yi ranar 6 ga watan Nuwamba.

A wani hukunci da ya yanke a yau Litinin Mai shari’a Inyang Ekwo, ya ce Uba bai taba zama dan takara ba, kasancewar ya fito daga zaben fidda gwani na  APC ba bisa ka’ida ba.

Alkalin kotun ya ce wanda ya shigar da karar, George Moghalu, ya yi nasarar tabbatar da cewa jam’iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba wanda Andy Uba ya yi ikirarin ya fito a matsayin dan takarar jam’iyyar.

Alkalin kotun ya umarci INEC da ta goge Uba daga tarihinta na tsayawa takara a zaben.

Daga nan sai ya umarci jam’iyyar APC da ta mayar wa mai kara kudin N22,500.000 da ya biya domin nuna sha’awa da fom na tsayawa takara tunda jam’iyyar ta kasa gudanar da sahihin zaben fidda gwani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here