Hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC ta ce jami’o’i 25 ne kawai a kasar nan ta tabbatar da ingancin kwasa-kwasai da suke yi dari-dari.
Hukumar ta NUC ta tabbatar da hakan A cikin “Kididdigan tsarin Jami’ar Najeriya na 2021” mai kwanan wata 11 ga Disamba, 2021.
Hukumar ta ce kasa da kashi 70 cikin 100 na kwasa-kwasan da jami’o’i ke yi suna samun karbuwa.
Solacebase ta ruwaito cewa a cikin wannan matsayi, jami’o’i 25 da suka sami cikakkiyar shaidar sun hada da Jami’ar Tarayya, Kashere dake Jihar Gombe, da Jami’ar Yusuf Maitama Sule, dake Jihar Kano, sai Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano, Wudil da sauran 22.
Sai dai babu daya daga cikin manyan jami’o’in da aka jera a cikin cibiyoyi 25 waɗanda ke da kwasa-kwasan karatunsu kashi 100.
A cikin darajar NUC kuma ta ƙididdige Jami’ar Ibadan (UI) a matsayin mafi kyawun ƙasar da maki 454.56.
Ga cikakken jerin jami’o’i 25 din
- Adeleke University, Osun State
- Al-Qalam University, Katsina State
- Caleb University, Lagos State
- Chrisland University, Lagos State
- Crescent University, Ogun State
- Federal University, Lokoja
- Federal University, Wukar
- Federal University, Kashere
- Hallmark University, Ogun State
- Hezekiah University, Imo State
- Ibrahim Babangida University, Niger State
- Igbenedion University, Edo State
- Kano University of Science and Technology, Kano
- Kebbi State University of Science and Technology
- Kogi State University
- Maitama Sule University, Kano State
- McPherson University, Ogun State
- Mountain Top University, Ogun State
- Niger Delta University, Delta State
- Nigeria Defence Academy
- PAMO University of Medical Science, River State
- Rivers State University
- Samuel Adegboyega University, Edo State
- Summit University, Kwara State
- Umaru Musa Yar’Ardua University, Katsina State.













































