Matatar mai ta Port Harcourt ta fara sarrafa danyen mai

Port Harcourt Refinery 1 750x430

 

Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya sanar da cewa matatar mai ta Port Harcourt, da ke Jihar Ribas, ta fara sarrafa danyen mai a hukumance.

Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na Kamfanin, Femi Soneye, ya bayyana wannan ci gaban a matsayin babban nasara ga ƙasar.

“A yau, Najeriya ta cimma babban gagarumin ci gaba yayin da matatar mai ta Port Harcourt ta fara sarrafa danyen mai. Wannan babbar nasara ce da ke nuna wani sabon shafin samun ‘yancin tattalin arziki da ci gaba ga ƙasarmu,” in ji Soneye a ranar Talata.

Ya jinjina wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Kwamitin Gudanarwar NNPCL, da kuma Babban Manajan Kamfanin, Mele Kyari, bisa ƙoƙarinsu wajen ganin an kammala wannan aikin.

Har ila yau, ya ce fara jigilar mai ta manyan motocin dakon kaya zai fara a yau, yayin da ake ci gaba da aiki tukuru domin dawo da ayyukan matatar mai ta Warri.

Duk da haka, wannan nasarar ta samu ne bayan da matatar ta kasa cika lokutan da aka sanya don fara aiki, ciki har da na watan Maris, Agusta, da Satumba na shekarar 2024.

Fara aikin matatar mai ta Fatakwal zai rage dogaro da shigo da kayayyakin man fetur daga ƙasashen waje, tare da habaka tattalin arzikin gida.

Karin bayani na tafe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here