Jami’ar Khalifa Isyaku Rabi’u (KHAIRUN) ta karbi sabbin dalibanta na shekarar 2024/2025 a ranar Litinin da ta gabata a wani biki da aka gudanar a harabar jami’ar da ke Kano.
SolaceBase ta ba da rahoton cewa taron, wanda ke nuna ƙwazo na musamman na jami’ar, ya nuna jajircewarta ga bada ilimi mai araha da kuma bada horo akan sana’o’in dogaro dakai.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Bilal Dahiru Tijjani, shugaban sashen kasuwanci, mataimakin shugaban jami’a Farfesa Abdulrashid Garba ya bayyana KHAIRUN a matsayin daya daga cikin manyan jami’o’in Najeriya masu zaman kansu masu saukin kudin makaranta, da ilimi mai inganci.
Garba ya lura cewa, hangen nesa na marigayi Khalifa Isyaku Rabi’u na samun ilimi yana ci gaba da wanzuwa ta hanyar barin tallafin karatu na rabin miliyan na cibiyar.