Jam’iyyar Labour Party reshen jihar Ogun ta kori babban daraktan kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa, Dakta Doyin Okupe bisa gaza sabunta katin shedar jam’iyyar sa cikin watanni shida da suka gabata.
Wannan na daga cikin kudurorin da aka cimma a karshen taron da suka gudanar a sakatariyar jam’iyyar da ke Abeokuta, inda suka bukaci da a samar da sabon darakta irin na tsattsauran ra’ayi na ‘yan Arewa domin nuna hali da daidaiton siyasar kasa.
An kori Okupe ne tare da sauran mutane dasuka hada da Abayomi Collins, Abel Olaleye, Jagun Lookman, Olori Oluwabukola Soyoye, Gbadebo Fesomade, (tsohon ma’ajin jihar), da Abdulmalik Olaleye (tsohon shugaban matasan jihar).
Sauran sun hada da Jide Amusan (Tsohuwar Sakatariyar Yada Labarai ta Jihar), Adeshina Wasiu Shojobi, Deborah Adewale, (Tsohuwar Shugabar Mata ta Jihar Ogun ta Gabas), da Olatunde Abolade (Tsohuwar Sakatariyar Jiha).
Ya ce matakin da suka dauka ya zama wajibi domin tabbatar da da’a da dimokuradiyyar cikin gida akoda yaushe.
Daganan yakuma zargi Okupe da karkatar da jam’iyyar Labour a jihar Kudu-maso-Yamma ta hanyar amfani da ‘yan PDP dan farfado da jam’iyyar, ba wai kawai jam’iyyar Labour ba.