Mun yi wa abokan hamayya kwanton-ɓauna muka ci zabe – Sanata Abdullahi Adamu

APC National Chairman Abdullahi Adamu
APC National Chairman Abdullahi Adamu

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce kayin da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka sha a mazabu ko jihohinsu na asali a zaben shugaban kasar da aka kammala na cikin salo ko dabarar zabe da jam’iyyar ta yi wajen samun nasara.

Ƴan Najeriya da dama sun yi mamakin yadda jiga-jigan APC suka kasa cin mazabu da jihohin nasu, ciki har da shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda jam’iyyar PDP ta masa kayi a Katsina.

Sai kuma shugaba mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, da kuma Sanata Abdullahi Adamu wadanda jam’iyyar Labour ta kayar a jihar Lagos da Nasarawa.

Hakazalika jam’iyyar Labour ta cinye jihar Filato, wadda gwamnan jihar Simon Lalong shi ne darakta-janar na yaƙin neman zaben ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

To sai dai Sanata Abdullahi Adamu, ya ce da sanin su suka bari abokan hammayar tasu suka samu galaba a wasu jihohin.

Ya ce “Ai shi abokin adawa a tafiya irin wannan sai ka yi masa kwanciyar Namaledu. Inda yake ganin ci ba a nan cin yake ba, Najeriya tana da fadi, mun faɗi a Legas ba mu so haka ba, shi ke nan sai suka mike kafa.”

Ya kara da cewa, “Mun fadi a Kaduna, ba mu so haka ba, Kano ba mu samu yadda muke so ba, Katsina suna yekuwar sun yi nasara, ni ma ina shugaban jam’iyya sun ci jihata, to sai muka bi a hankali muka yi musu yankan baya.”

Shugaban jam’iyyar APC ya ce babu wani abin kunya a cikin kayen da aka yi wa jiga-jigan nasu tun da sun samu abin da suke so.

Dangane da shawarar da masana suke bayarwa cewa akwai bukatar shugaba mai jiran gado, Bola Ahmed Tinubu, ya shigar da abokan hamayyarsa a cikin gwamnatin da zai kafa kuwa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce akwai lokacin da ya kamata a yi hakan amma sai bayan an kammala shari’ar zabe:

“Akwai lokutan da za ka nemi abokan adawa ka yi zama da su, amma yanzu ba a ma gama fita ruwa ba tun da akwai zabe na gwamnoni, za mu kara samun fahimtar inda Najeriya ta nufa.”

A cewar shugaban jam’iyyar APC, nasarar da jam’iyyarsu ta samu a zaben shugaban ƙasa ta ba su kwarin gwiwa cewa za su tabuka abin kirki a zaben gwamnonin da ke tafe:

Ya ce, “Juma’a mai albarka tun daga Laraba ake gani. Yadda muka ci zaben shugaban kasa haka za mu ci na jihohi. Ba za mu ci duk jihohin Najeriya ba. Ba za mu so mu cinye duka ba, don sai a ce muna da hadama.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here