Shahararren malamin addinin Musulunci, Youssef al- Qaradawi wanda ke cikin kusoshin kungiyar Muslim Brotherhood ya rasu.
Tsohon shugaban kungiyar kuma Limaman Musulunci na duniya ya rasu ne yana da shekaru 96.
An haife shi a Masar kafin ya koma Qatar da zama.
Youssef al- Qaradawi ya wallafa litattafan musulunci da dama.
Yana gabatar da shirin talabijin a tasha al-Jazeera kuma miliyoyin mutane ne ke bin wa’azinsa a fadin duniya.
(https://www.aljazeera.com/)












































