Ba zai yi wu a saki Bazoum a lokacin da kasashen duniya ke ta kiraye-kirayen a sake shi ba- Tchiani

download
download

Jagoran gwamnatin soji a Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya ce akwai dalilan da suka sanya su kin sakin hambararren shugaban kasar, Mohammed Bazoum.

Janar Tchiani ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kafar yada labarai ta gwamnati ranar Lahadi.

Lamarin na zuwa ne dai-dai lokacin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta ce za ta wakilta wata tawaga da zata kara tattaunawa da jagororin mulkin sojin na Nijar.

Tattaunawar da ake sa ran zata warware dambarwar da ake ciki tun bayan juyin mulkin a watan Yuli.

Tun farko, ECOWAS ta yi barazanr daukar matakin soji a kan Jamhuriyar Nijar matukar sojojin suka gaza mayar da Bazoum kan mulki.

Sai dai sojojin sun ki bin umarnin, lamarin da ya sa kungiyar ta ki cire takunkuman da ta kakaba wa mata tun farko.

Karanta wannan:A buga sunayen wadanda aka kashe, sannan a biya iyalansu diyya-Jam’iyyar LP

Sai dai a tattaunawar da ya yi da kafar yada labarai ta RTN, Shugaba Tchiani yace rashin tsaro na cikin dalilan da suka sa su kin sakin Bazoum din.

Tchiani ya ce ba zai yi wu a saki Bazoum a lokacin da kasashen duniya ke ta kiraye-kirayen a sake shi ba, saboda barazanar tsaro.

Mohammed Bazoum Niger Republic

Yayin taron da ta gudanar a Abuja ranar Lahadi, Ecowas ta ce za ta duba yiwuwar rage takunkuman da ta sanya wa Nijar.

A cewarta amma sai sojoji sun amince za su mayar da mulki ga farar hula cikin kankanin lokaci.

Shugabannin kasashen Benin da Saliyo da Togo ne za su jagoranci tattaunawar, inda za su matsa wa sojojin na Nijar lamba don su amince da batun.

A baya bayan nan ne, Burkina Faso, da Nijar, da Mali suka amince da kulla wani kawancen tsaro da kuma hadaka ta siyasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here