Hukumar Shirya Jarabawar Kasa (NECO) za ta fitar da sakamakon Jarabawar Shaidar Kammala Sakandare (SSCE) ta shekarar 2026 a ranar Alhamis, 24 ga Satumban 2026.
A cewar wata takarda da aka fitar a ranar Talata, za a sanar da sakamakon a da misalin karfe 11 na safe a hedikwatar NECO da ke Kilomita 8, Titin Bida Minna a Jihar Neja.”
Read also: UTME: Hukumar JAMB ta gargadi masu yin jarrabawa da su kula da shafukan boge
Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwar NECO, Farfesa Dantani Wushishi, ne ya jagoranci taron Kwamitin Bayar da Shaidar SSCE na 2026 a ranar Talata a hedikwatar hukumar.
Read also: Labarai cikin hotuna: Shugaban majalisar wakilai ya kuma aji a jami’ar Harvarda domin karo karatu
A wani sako da hukumar ta wallafa a shafin X ta ce taron ya zama matakin karshe na shirye-shirye kafin fitar da sakamakon a hukumance.
Ana gudanar da jarabawar SSCE a duk shekara ga daliban da ke shekarar karshe a sakandare.
An gudanar da jarabawar daga 15 ga Yuni zuwa 23 ga Yulin 2026.












































