JNI ta yi tir da karuwar rashin tsaro a Najeriya, ta bukaci daukar mataki na gaggawa

Sultan of Sokoto Muhammad Saad Abubakar III 666x430

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta yi tir da tabarbarewar yanayin tsaro a fadin Najeriya, inda ta bayyana damuwarta kan ci gaba da kashe-kashe, garkuwa da mutane, hare-haren ‘yan ta’adda, fashi da makami da raba al’ummar da basu ji ba ba su gani ba da muhallansu.

Wannan kira na kunshe ne cikin wata sanarwa da helkwatar kungiyar JNI ta kasa da ke Kaduna ta fitar a ranar Laraba, wanda Sakataren kungiyar, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ya sanya wa hannu, a madadin shugabancin kungiyar karkashin Shugaban Majalisar Koli kuma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.

JNI ta bayyana cewa jihohi da dama da suka hada da Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna, Kebbi, Borno, Yobe, Adamawa, Niger, Gombe, Kogi, Benue da Plateau, suna fuskantar tashe-tashen hankula na rashin tsaro da suke jawo asarar rayuka, garkuwa da mutane, raunuka, satar shanu da kuma hare-hare kan al’ummomi.

Kungiyar ta nuna damuwarta cewa duk da ayyukan soja da na jami’an tsaro da ake ci gaba da yi, har yanzu ana kashe ‘yan Najeriya, ana garkuwa da su, ana raba su da muhallansu, yayin da wasu da dama ke rayuwa cikin fargaba da tashin hankali na dindindin.

“Duk da rahotannin da ke cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan soja da na tsaro, har yanzu ana kashe ‘yan kasa, ana garkuwa da su, ana raba su da muhallansu, sannan ana sanya su cikin tsoro da firgici,” in ji sanarwar.

Haka kuma, JNI ta ambaci ayyukan soja na baya-bayan nan inda aka ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su, sannan aka kama mutane hudu da ake zargi da mambobin kungiyar ta’addanci ta Lakurawa ne.

Ta kara da cewa kungiyoyin Boko Haram da ISWAP na ci gaba da kai hare-hare kan al’ummomin da ba su da kariya, sannan suna kalubalantar hukumomin tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas.
Game da rahoton mutuwar mutane 37 a hannun jami’an tsaro Civil Defence bayan kama su da laifin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar Neja, JNI ta bukaci a gudanar da bincike na gaskiya, mai zaman kansa kuma na amana.

Kungiyar Musuluncin ta yi maraba da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na dakatar da wasu jami’ai har sai an kammala bincike, amma ta nuna damuwa game da yanayin tsare mutane, samun kulawar lafiya da kuma sanya ido kan wadanda ake tsare da su.

Ta ce zanga-zangar da jama’a suka yi a Minna, babban birnin jihar Neja, kan lamarin na nuni da girman damuwar da ake da ita game da amincewa da hukumomin tsaro.

JNI ta yi tir da kisa da garkuwa da mutane marasa laifi, tana mai jaddada cewa ta’addanci, fashi da makami, ayyukan laifi, tsanani da tashe-tashen hankula na kabilanci ko na al’umma ba su da wata hujja aikata su.

A cewar kungiyar, Musulunci ya ba da daraja mai yawa ga ran dan adam, kuma “babu wata matsala, akida ko matsananciyar damuwa da ke halatta ta’addanci ko kisan mutane da gangan da ba su ji ba ba su gani ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here