NDC za ta dawo da tallafin man fetur – Kwankwaso

WhatsApp Image 2026 04 11 at 22.25.11 750x430 (1)

Dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyar za ta dawo da tallafin man fetur ta wata hanya daban idan an zabe ta a 2027.

Da yake jawabi a wata hira da Arise News, tsohon Gwamnan Jihar Kano ya ce NDC za ta dauki wata hanya daban ta tallafi, ciki har da fadada tace yawan mai a cikin gida.

“Za mu dawo da tallafi ta hanyar da muke ganin ta dace,” in ji shi.

“Akwai hanyoyi da yawa, zan iya fada muku daya yanzu. Muna da matatar mai da wani dan kasuwa ya gina, kuma ina da tabbacin za a gina karin matatun mai.

“Yanzu, idan daidaikun mutane a wannan kasa za su iya gina matatun mai, ban ga dalilin da zai sa gwamnati, a karkashin kowani yanayi da ba za ta gina matatar mai ko matatun mai ba har a cimma mafi karancin bukata.

“Menene mafi karancin bukata? Mafi karancin bukata shi ne mutane a fadin kasar su je gidajen mai su sayi man fetur a farashi mai sauki.

“Mu a NDC za mu yi duk abin da ya kamata don rage farashin mai.”

Kwankwaso ya ce manyan ‘yan takarar shugaban kasa uku a zaben 2023 sun yi alkawarin cire tallafin amma ya soki Shugaba Bola Tinubu saboda cire shi nan take bayan ya hau mulki.

Ya ce matakin ya taimaka wajen tabarbarewar tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

“A 2023, lokacin yakin neman zabe, na tunawa cewa duk su ukun dukansu sun ce za su cire tallafin. A hakika, kafin nan, Atiku ma ya kara da cewa zai sayar da duka matatun mai guda hudu ga abokansa,” in ji shi.

“Daga cikin su ukun, Bola Tinubu ya dauki matakin cire tallafin, kuma sakamakon da muka yi tunanin zai faru tabbas ya faru.

“Ba wai kawai ya dauki matakin cire tallafin ba, abin da ya yi shi ne ya cire shi nan take, a gaskiya, a ranar farko, ba tare da duba duk wata matsala da za ta iya biyo bayan hakan ba.

“Kuma haka muka tsinci kanmu a cikin wannan tabarbarewar tattalin arziki. Yanzu, kowa ya gane cewa kuskure ne.”

Kwankwaso ya kuma zargi dan takarar jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, da yin alkawarin cire tallafin saboda siyasa.

Ya ce Atiku, wanda ya kasance dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023, yana neman yin amfani da damuwar jama’a ta hanyar yin alkawarin da a baya zai iya cikawa ba, ba tare da bayyana yadda za a samar da manufar ba.

“Amma abin da Wazirin Adamawa ya yi kawai siyasa ce. Ba na tunanin yana nufin abin da ya fada,” in ji Kwankwaso.

“Wannan na farko kenan. Na biyu kuma na biyu, bai fada wa kowa yadda zai yi ba.

“Amma ya san mutane yanzu suna cikin tsananin bukata, idan kawai ka fito waje ka ce, ‘Zan cire shi, koda kuwa ka fada sau da yawa cewa ba za ka cire shi ba.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here