DA DUMI DUMI: Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da zabukan da bangaren Ganduje suka yi

A9972A6E 1971 4167 82E0 DB065047FABE
A9972A6E 1971 4167 82E0 DB065047FABE

A yau Alhamis ne bangaren kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun birnin tarayya ta yanke wanda ya soke zaben mazabu dana kananan hukumomi na jam’iyyar APC a jihar Kano.

Kotun daukaka kara ta ce karamar kotun ba ta da hurumi.

Solacebase ta ruwaito cewa bangaren Ibrahim Shekarau ya garzaya babbar kotun tarayya dake babban birnin tarayya Abuja bayan zabukan na jam’iyyar APC a Kano, inda kotun ta amince da zabukan da bangaren Shekarau suka gudanar gudanar sabanin na bangaren gwamna Ganduje.

Rashin gamsuwa da hukuncin da babbar kotun ta yanke ya sanya bangaren gwamna Ganduje suka garzaya zuwa kotun daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.

Kotun daukaka kara ta kuma bayyana cewa batu ne na cikin gida na jam’iyya mai mulki, don haka Shugabannin jam’iyyar ne ya kamata su yanke hukunci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here