UNGA81: Gwamnonin Arewa maso Yammacin Najeriya sun kuduri aniyar hada gwiwa don zaman lafiya

UNGA North 750x430

Gwamnoni bakwai na shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya sun himmatu wajen ciyar da tsarin hadin gwiwa na shiyyar gaba daya domin samar da zaman lafiya, juriya da damarmakin tattalin arziki a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 (UNGA81) na shekarar 2026.

Shirin Raya Kasashe na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata cewa gwamnonin sun gana a wani taro na musamman a birnin New York wanda Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Yamma (NWGF) ta shirya tare da hadin gwiwar UNDP.

Gwamnonin sun yi kira da a karfafa gwiwar abokan hadin gwiwa na kasa da kasa, kudaden raya kasa da zuba jari domin cin moriyar tsarin zaman lafiya, tsaro da raya kasa na Arewa maso Yamma (2026–2030) ya zama a aikace.

Babban taron ya hada da gwamnonin, jami’an Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin Mataimakiyar Sakatare Janar, Amina Mohammed, abokan ci gaba, cibiyoyin kudi na kasa da kasa, shugabannin kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyin agaji da mambobin kungiyoyin diflomasiyya.

Masu jawabi da mahalarta taron sun amince da matsaya guda ‘samar da zaman lafiya mai dorewa yana bukatar zuba jari a cikin al’amura da za su ba wa mutane, garurwa da tattalin arziki damar bunkasa.’

Wannan sadaukarwa ta gwamnonin tana nuna sauyi daga rarrabuwar kawuna wajen tunkarar matsaloli zuwa ga tsarin hadin gwiwa na shiyya daya.

Jihohi bakwai din da suka hada da Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara – sun haduwa a karkashin tsari guda domin magance rashin tsaro da rauni ya yin da suke fadada hanyoyin rayuwa, ayyukan yi, ayyukan more rayuwa da damarmakin tattalin arziki.

Shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya, wadda ke da mazauna fiye da miliyan 60, tana da muhimmanci sosai ga tsarin abinci na Najeriya, kasuwancin cikin gida da na shiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here