Dalilan da suka sa dole Najeriya ta gyara tsarin tuntubar manoma

IMG 20260913 WA0460 678x430

Fafutukar da Najeriya ke yi don tabbatar da wadatar abinci ba kawai matsalar yawan abin da manoma ke samarwa ba ne. Matsala ce kuma ta yadda ilimi, fasaha da tallafin kwararrun masana ke isa ga mutanen da ke samar da abinci ga kasar.

Hakan ce tasa tsarin tuntubar manoma ya cancanci a ba shi fifiko fiye da yadda ake ba shi a yanzu.

Ga miliyoyin manoman Najeriya, musamman kananan manoma a yankunan karkara, jami’in tuntubar manoma shi ne a mafi yawon lokuta ya ke zama hanyar hada binciken kimiyyar noma da abin da ke faruwa a gona. Wadannan ayyukan tuntubar manoma na iya taimaka wa manoma su fahimci ingantaccen iri, yadda ake sanya taki, magance kwari da cututtuka, hanyoyin noma na zamani da suka dace da sauyin yanayi, kula da amfanin gona bayan girbi da kuma sabbin fasahohi.

Lokacin da wannan hanyar hadin ya yi rauni, jarin da aka zuba a harkar noma na iya gaza cimma cikakkiyar nasara.

Najeriya ta kwashe shekaru tana kaddamar da shirye-shiryen noma, tana rarraba kayan aiki, da kuma tallafa wa manoma ta hanyoyi daban-daban, amma rarraba ingantaccen irin shuka, misali, ba yana nufin lallai manomi ya san hanyar da ta dace ya yin shukarsa ba, tazarar da ke tsakanin shukoki, yadda ake zuba taki, ko dabarun magance kwari da ake bukata don samun amfanin da ake bukata.

Wannan shi ne daidai inda tsarin tuntubar manoma dake aiki yake da muhimmanci.

Duk da haka, tsarin tuntubar manoman Najeriya ya dade yana fuskantar kalubale na rashin isassun ma’aikata da kayan aiki. Hukumar Bincike da Sadarwa ta Kasa kan Noma (NAERLS) ta bayyana cewa akwai babban gibi tsakanin yawan manoma da jami’an tuntuɓar manoma da ake da su. Wannan gibi na nufin jami’in tuntubar manoma guda daya na iya zama mai alhakin kula da dubbannin manoma, wanda hakan ke sa aikin tuntubar juna akai-akai kuma mai ma’ana ya zama mai matukar wahala.

Sakamakon haka shi ne, ana samun tsarin da manoma ke iya karbar kayan tallafin noma ba tare da sun sami isasshen tallafin fasaha na yadda za su yi amfani da su yadda ya kamata ba.

Halastacciyar Dama

Kudurin Dokar Farfado da Ayyukan Tuntubar Manoma (Agricultural Extension Services Revitalisation Bill) da ke gaban Majalisar Tarayya a yanzu ya ba da damar magance wasu daga cikin wadannan matsaloli na tsarin gudanarwa.

Kudurin ya riga ya tsallake karatu na farko a dukkannin Majalisun Dattawa da Majalisar Wakilai. Matakan majalisa da suka rage, ciki har da taron sauraron jin ra’ayin jama’a, za su kasance masu muhimmanci domin suna ba da damar ’yan majalisa su ji kai-tsaye daga bakin manoma, kwararrun masana harkar tuntubar manoma, masu bincike da sauran masu ruwa da tsaki kafin a kammala dokar.

Sanata Saliu Mustapha ne ya gabatar wannan doka a Majalisar Dattawa. Bayanan jama’a kan kudurin dokar sun kuma nuna Kungiyar Ci Gaban Mata Manoma (WOFAN), ta hanyar shirye-shiryen ta na noma da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, a matsayin daya daga cikin kungiyoyin da ke tallafa wa kokarin sake fasalin tsarin tuntubar manoma. Ita kanta WOFAN ta fito fili ta bayyana kanta a matsayin daya daga cikin kungiyoyin da ke hada gwiwa da masu ruwa da tsaki, abokan hulda na kamfanoni masu zaman kansu, da kungiyoyin manoma kan wannan doka da aka gabatar. Wannan rawar da suke takawa ya cancanci a yaba da ita.

Tambayar da ke gaban Najeriya a bayyane take; shin kasar za ta iya ci gaba da kokarin sauya harkar noma ba tare da ta gyara tsarin da ke da alhakin kai ilimin noma da sabbin fasahohi ga manoma ba?
Amsar ita ce a’a.
Tuntubar Manoma Ya Wuce Kawai Koya Wa Manomi Aikin Noma

Kada a mayar da tsarin tuntubar manoma na zamani zuwa kawai ga jami’i ya ziyarci kauye don gaya wa manoma lokacin da za su yi shuka.

Noma ya sauya.

Manoma na kara bukatar bayanai game da yanayi, kasuwanni, kudi, injiniyan noma, ingantattun iri, lafiyar kasa, hadarin sauyin yanayi, sarrafa amfanin gona, adana kaya da tsarin samar da daraja. Matasan da ke shiga harkar noma su ma suna bukatar dabarun kasuwanci da na zamani na na’ura mai kwakwalwa idan ana son noma ya zama sana’a mai kawo riba maimakon kawai hanyar dogaro da kai na abincin yau da kullum.

Don haka, kudurin dokar da aka gabatar ya cancanci kulawa ba wai kawai don zai iya samar da tsarin shari’a ga ayyukan tuntubar manoma ba, a’a, har ma saboda zai iya taimakawa wajen sake fassara ma’anar tuntubar manoma a harkar noman Najeriya na zamani.

Yakamata tsarin tuntubar manoma ya hada manoma da masu bincike, kasuwanni, hukumomin kudi, masu samar da fasaha da shirye-shiryen gwamnati.

Kuma yakamata ya yi aiki ta ɓangarori biyu.

Kada manoma su zama kawai masu karbar bayanai daga masu bincike da gwamnati. Abubuwan da suke fuskanta a aikace ya kamata su rika fadakar da bincike da manufofin noma na gwamnati. Manomin da ke fama da sabon kwaro, sauyin yanayin ruwan sama, ko wahalar samun wani takamaiman kayan aiki, yana da bayanan da masu tsara manufofi da masu bincike ke bukata.

Kyakkyawan tsarin tuntubar manoma yana samar da wannan dangantaka ta bangarori biyu.
Matsalar Ma’aikata
Babu wani sauyin tsarin tuntubar manoma da zai yi nasara ba tare da an magance matsalolin mutanen da ake sa ran za su kiyaye shi ba.

Ma’aikatan tuntubar manoma suna bukatar horon kwararru, motoci ko baburan zirga-zirga, kayan aiki, kayan aiki na zamani na na’ura da kuma damar akai-akai don sabunta iliminsu.

Suna kuma bukatar adadin manoma da za su iya kulawa da su cikin sauki.

Fasaha na iya taimakawa wajen cike gibin, amma ba za ta iya maye gurbin ayyukan dan adam ba gaba daya. Manomin da ke da iyakacin damar shiga yanar gizo, rashin ilimin na’urar zamani, ko matsalar fasaha da ke bukatar duba ta, sanya ido, har yanzu yana bukatar kwararren mutum wanda zai iya fahimtar yanayin kuma ya ba shi jagora na zahiri.

Don haka, ya kamata Najeriya ta bi tsarin hadin gwiwa.

Hanyoyin sadarwa na zamani, wayoyin salula, kirkirarriyar basirar dan adam (AI), rediyo da sauran hanyoyin sadarwa na iya fadada isar ayyukan tuntubar manoma. Amma wadannan sun kasance masu karfafa tsarin ma’aikatan tuntubar manoma maimakon su zama dalilan gwamnatoci na yin watsi da su.

Mata da Matasa Manoma Suna da Muhimmanci

Dole ne tsarin tuntubar manoma na kasa ya amince da banbancin da ke tsakanin manoman Najeriya.

Mata suna da babban kaso a cikin samar da amfanin gona, yayin da ake kara karfafa gwiwar matasa su kalli noma a matsayin kasuwanci da hanyar samun aiki.

Duk da haka, ba duka manoma ke da dama daya ta samun fili, kudi, fasaha, kasuwanni ko bayanai ba.

Don haka, dole ne a tsara shirye-shiryen tuntubar manoma don su isa ga mata, matasa manoma, da mutane a yankunan karkara masu nisa, maimakon tunanin cewa tsari iri daya na gamayya zai yi aiki a ko’ina.

Kudurin dokar da aka gabatar ta janyo hankali da tallafi saboda damarsa ta karfafa ayyuka ga kananan manoma da kuma inganta daukacin tsarin noma. WOFAN kuma ta jaddada cewa dokar na iya inganta ayyukan tuntubar manoma da kuma yanayin aiki ga ma’aikatan tuntubar manoman.

Wadannan batutuwa ne da ya kamata a yanzu a fuskantar, amma ya kamata jama’a da majalisa su bincike su gaba daya.

Sallake karatu na biyu na dokar matakin farko ne kadai

Kada Majalisar Tarayya ta dauki amincewa da dokar tuntubar manoma a matsayin karshen matsalar.

Najeriya na da isassun manufofin noma, raunin da ake samu akai-akai shine rashin aiwatarwa.

Idan kudurin ya zama doka, tambayoyi na gaba za su kasance game da kudade, ma’aikata, hadin gwiwa, rikon amana da sakamako na gaske da za a iya aunawa.

Waye zai dauki ma’aikata kuma ya horar da ma’aikatan tuntubar manoman?

Yaya tsarin gwamnatin tarayya da na jihohi za su yi aiki tare?

Ta yaya ayyukan tuntubar manoma za su isa ga yankunan karkara ddake nesa?

Ta yaya gwamnati za ta auna ko manoma suna karbar shawarwari masu amfani da gaske?

Ta yaya za a hada fasaha ba tare da an ware manoman da ba su da damar shiga yanar gizo ba?

Kuma, watakila mafi mahimmanci, nawa ne gwamnatoci za su shirya don warewa domin tabbatar da tsarin ya yi aiki?

Ya kamata a amsa wadannan tambayoyin kafin shagalin biki da yawanci ke biyo bayan tsallakewar doka.

Kalubalen samar da wadataccen abinci ga Najeriya yana bukatar fiye da tallafin gaggawa da rarraba kayan noma na lokaci-lokaci. Manoma suna bukatar samun ilimi da tallafi mai dorewa.

Kudurin Dokar Farfado da Ayyukan Tuntubar Manoma ya ba da damar ƙarfafa wannan hanyar hadi da ta bace.

Ya kamata Majalisar Tarayya ta yi amfani da taron sauraron jin ra’ayin jama’a da matakan majalisa don inganta dokar inda ya dace, ta saurari mutanen da za su dogara da ita, kuma ta tabbatar da cewa duk abin da ya zama doka a karshe ya kasance mai saukin aiki, mai tallafi mai kyau da kuma ikon samar da sakamako na gaske.

WOFAN da sauran masu ruwa da tsaki na iya ci gaba da fafutukar kafa dokar, kamar yadda bayanan su na fili suka nuna. Amma a karshe, nauyin yana wuyan gwamnati.
Najeriya ba za ta iya sauya harkar noma ba yayin da take barin manomanta ba tare da ingantaccen tsarin samun ilimin da ake bukata don sauya gonakansu ba.

Don haka, gyaran tsarin tuntubar manoma ba karamin batu ba ne a cikin muhawarar wadatar abinci ta ƙasar.
Yana daga cikin mafita.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here