Farashin fetur a Najeriya ya fi na Amurka, Ghana, Afirka ta Kudu da sauran kasashe sauki — Minista

Pump price

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Heineken Lokpobiri, ya ce matsakaicin farashin man fetur a Najeriya ya kasance kasa da na Amurka, Ghana, Kamaru da Afirka ta Kudu duk da cire tallafin.

Lokpobiri ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television a ranar Talata, yayin da yake kare matakin gwamnatin tarayya na soke kayyade farashin man fetur a cikin fargabar da ake da ita game da tsadar farashinsa.

A cewarsa, a halin yanzu ana siyarda man fetur a kusan Naira 1,430 kowace lita a Najeriya, idan aka kwatanta da kusan Naira 1,633 a Amurka, Naira 1,959 a Kamaru da Naira 2,070 a Ghana da Afirka ta Kudu.

“Kun san nawa ne matsakaicin farashi a Amurka, litar mai 1,633 ce. A Najeriya, 1,430 ne. Idan ka je Kamaru, 1,959 ne. Idan ka je Ghana 2,070 ne. Idan ka je Afirka ta Kudu 2,070 ne. Don haka matsakaicin farashin man fetur a Najeriya kan kowace lita har yanzu ya fi sauki,” in ji shi.

Kalaman nasa sun zo ne yayin da Matatar Mai ta Dangote da sauran ‘yan kasuwar man fetur suka rage farashi biyo bayan raguwar farashin danyen mai a duniya.

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga N1,350 zuwa N1,325 kowace lita, yayin da sauran ‘yan kasuwa ma suka sanar da rage farashi a Legas, Fatakwal, Calabar da Warri.

Duk da raguwar, har yanzu ana sayar da man fetur tsakanin N1,370 zuwa N1,450 a kowace lita a wasu wurare.

Lokpobiri ya ce kasancewar Najeriya kasa mai arzikin mai da kuma samun matatar mai ta Dangote ba ya nufin lallai farashin fetur zai ragu ta kowace hanya, yana mai jaddada cewa ana cinikin kayayyakin mai ne a kasuwa mai zaman kanta.

Ya bayyana cewa tsarin soke kayyade farashin ya ƙarfafa gwiwar masu zuba jari na kudi masu zaman kansu a fannoni daban-daban na man fetur, inda ya bayar da hujjar cewa matatar man fetur ta Dangote za ta sha wahala wajen yin gogayya idan da ace gwamnatin tarayya ta ci gaba da shigo da fetur tare da sayar da shi kasa da farashin da ake da shi a kasuwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here