Kisan Uromi: DSS ta kama wasu manyan mutane biyu da ake zargi da hannu 

DSS3

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama wasu manyan mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kashe matafiya 16 a Uromi, karamar hukumar Esan Arewa maso Gabas ta jihar Edo a makon jiya.

Babban Sakataren Yada Labarai na gwamnan, Friday Ituah, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a garin Uromi bayan samun sahihan bayanan sirri.

A cewarsa, jami’an hukumomin tsaro daban-daban na farautar wasu manyan mutane da ake zargi da hannu a cikin lamarin.

Karin karatu: CISLAC ta yabawa gwamnan Edo kan ziyarar jaje zuwa Kano, da dakatar da kungiyoyin ‘yan banga

Ituah ya bayyana cewa an garzaya da su Abuja domin ci gaba da yi musu tambayoyi da kuma gurfanar da su a gaban hukumomin da abin ya shafa.

A ranar Litinin ne gwamnan jihar, Sanata Monday Okpebolo ya kai ziyarar jaje jihar Kano, har ma ya bayyana cewa tuni aka kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da yi musu tambayoyi.

Gwamna Okpebholo, wanda ya ziyarci jihar domin jajantawa gwamnati da iyalan wadanda aka kashe, ya sha alwashin cewa za a yi adalci, kuma za a gurfanar da wadanda ke da hannu a kisan.

Gwamna Okpebholo ya kuma tabbatar wa iyalan wadanda abin ya shafa cewa za a biya isassun diyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here