Sanata Natasha Akpoti-Oduaghan ta yi zargin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya bai wa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kwangila domin shirya yadda za a kashe ta.
Akpoti-Uduaghan ta yi wannan zargin ne a lokacin da take jawabi ga al’ummar mazabar ta a wani taron gangami da aka gudanar a Ihima da ke jihar Kogi ta tsakiya a ranar Talata.
Ta ce da farko Akpabio ya tuntubi Usman Ododo domin ya fara kiran ta, amma gwamnan jihar mai ci “ya ce masa ba zai yiwu ba saboda talakawa na tare da ita.”
Ta ce Mista Akpabio, bai gamsu da martanin Ododo ba, ya roki Bello da ya tabbatar da kiran ta da kuma kashe ta, tare da alkawarin bayar da kudaden tafiyar da ayyukan.
Karanta:Cikin hotuna: Natasha Akpoti ta yi watsi da dokar hana fita, ta yi jawabi ga magoya bayanta a Kogi
Ta kara da cewa, “Akpabio ya ce wa Yahaya Bello ya kashe ni, Akpabio ya ce masa ya tabbatar cewa kashe ni bai faru a Abuja ba, ban bayyana hakan ba, amma ba mu sanar da ‘yan sanda ba.”
Yar majalisar dokokin Kogi ta tsakiya, wadda majalisar dattawa ta dakatar saboda rashin da’a a yayin zaman majalisar, ta zargi Akpabio da yunkurin yin lalata da ita.













































