‘Yan bindiga sunyi garkuwa da surukar farfesa Ango Abdullahi, tare da ‘ya ‘yan ta hudu a karamar hukumar Giwa da ke cikin Jihar Kaduna.
Ango Abdullahi wanda shine shugaban kungiyar dattawan Arewa ya tabbatarwa da manema Labarai a Zariya, ranar Laraba, cewa ‘yan bindigar sunyi garkuwa da surukar sa, Ramatu Samaila, tare da jikokin sa hudu, ranar Talata da daddare.
Ya kara da cewa matar dan nasa ‘ya ce ga mai unguwar Yakawada.
An tattaro bayanan cewa ‘yan bindigar sun mamaye karamar hukumar Giwa ranar Talata da daddare, inda kai tsaye suka shiga gidan mai unguwa nan ma sukayi garkuwa da wasu mutane a gidan.
Sanan kuma ‘yan bindigar sunyi garkuwa da mazauna kauyen wadan da suka hada da Abubakar Mijinyawa tare da matan sa biyu, Aisha da kuma Hajara.
A baya dai ‘yan bindigar sunyi garkuwa da dan Abdullahi, wato Sadiq Ango Abdullahi, wanda yana daya daga cikin wanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, daga baya kuma aka sake shi bayan an biya masa kudin fansa.
Sai dai har yanzu jami’an ‘yan sanda basu ce komai ba akan faruwar lamarin.













































