Rundunar yan sandan kano ta yi nasarar dakile yunkurin garkuwa da wani dagaci.

Nigerian police patrol1
Nigerian police patrol1

Aminu Bala Madobi-Daga Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta ce ta dakile wani yunkurin yin garkuwa da Dagacin Garun-Babba, Malam Abdulmuminu Mudi da ke karamar hukumar Garun-Mallam a jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan kano, SP Abdullahi Haruna-Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

“Bayan samun rahoton, mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda na rundunar, DCP Abubakar Zubairu, ya tara tawagar ‘yan sanda da kuma rundunar yaki da masu garkuwa da mutane.

Haruna-Kiyawa ya bayyana cewa rundunar ashirye take dan zakulo wadanda suka aikata laifin.

“Saboda haka, masu garkuwa da mutanen yayin bata-kashin bar Dagacin kauyen da babura uku.

“An ceto wanda akayi Shirin daukewa ba tare da jin ko da rauni ba, kuma babura uku day masu laifin ke amfani da su, ‘yan sanda sukai nasarar kwato su,” inji shi.

Mukaddashin kwamishinan ‘yan sanda na rundunar ya yabawa jami’an ‘yan sandan bisa halin jarimta dasuka nuna, sannan ya umarce su da su kara kaimi wajen kamo wadanda ake zargi sun tsere yayin faruwar lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here