Cikin hotuna: Natasha Akpoti ta yi watsi da dokar hana fita, ta yi jawabi ga magoya bayanta a Kogi

Natasha Akpoti new 750x430

Sanata mai wakiltan Kogi ta tsakiya wadda aka dakatar Natasha Akpoti-Uduaghan, ta bijirewa dokar hana zirga-zirgar da aka sanya wa jihar Kogi inda ta gudanar da taron ta a mahaifarta.

Ƴar majalisar ta samu tarbar jama’a da murna a karamar hukumar Okehi.

Dawowar ta na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar Kogi ta haramta tarukan jama’a da tarukan da ake zargin na da alaka da tsaro.

Amoka Monday, shugaban karamar hukumar Okehi, ya ayyana dokar hana fita a fadin karamar hukumar.

“Babu wanda zai hana ni dawowa gida. Ni mutuniyar Ebira ce; wannan ita ce ƙasata,” in ji ta cikin harshen Ebira.

Labari mai alaƙa: Yan sanda sun dakatar da Natasha daga zagayen Sallah da za ta yi a Okene

“Ni diyar marigayi Jimoh Abdul Akpoti ce, na san tushena, kuma ba na tsoron kowa.”

Zuwan ta ya biyo bayan gargadin da rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta yi mata da ta soke taron da ta shirya yi na bikin Eid-el-Fitr a gundumar.

Natasha Akpoti ta yi fatali da dokar hana fita don ta yi wa magoya bayanta jawabi a Kogi.

Kafin zuwanta, Sanatan ta yi zargin cewa duk wani tashin hankali a yayin taron ya kamata a dora wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo, da kuma Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here