Tsohon babban Hafsan tsaron Najeriya Christopher Musa ya gana da Tinubu a fadar Aso

General Christopher Musa

Tsohon babban Hafsan tsaro na ƙasa janar Christopher Musa ya gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja a ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa Janar Musa ya isa fadar gwamnatin da misalin ƙarfe 7:03 na yamma, inda wani jami’in tsaro ya raka shi zuwa wajen ofishin shugaban ƙasa domin ganawa.

Tsohon babban Hafsan ya je ne sanye da riga mai duhu, kuma wannan shi ne karo na farko da yake ganawa da shugaban ƙasa tun bayan ritayersa a ranar 24 ga Oktoba 2025.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a bayyana takamaiman dalilin ganawar ba, domin ba a fitar da cikakken bayani kan abinda suka tattauna ba.

Ana dai ganin ganawar ba ta rasa nasaba da ƙarin tabarbarewar tsaro a ƙasar musamman a yankunan Arewa, ciki har da sace ɗalibai a Jihar Kebbi, harin da aka kai wa masu ibada a Eruku ta Jihar Kwara, da kuma garkuwa da yara a makarantar Katolika da ke Minna a Jihar Neja.

A halin yanzu shugaban ƙasa Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro, inda hukumomin tsaro suka ƙara tsananta yaki da ta’addanci da kuma garkuwa da mutane a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Hukumomin tsaro suna ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here